IQNA

Wata Mata 'Yar Kasar Morocco A Ziyarar Arbaeen

22:46 - November 20, 2016
Lambar Labari: 3480958
Bangaren kasa da kasa, wata mata 'yar kasar Morocco ta halarci taron arbaeen na Imam Hussain (AS) a Karbala na wannan shekara.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labarai na hubbaren Imam Hussain (AS) cewa, matar mai suna Fatima Mubarak ta halarci tarukan na bana da ake gudanarwa a birnin na karbala mai alfarma.

A znatawar ta da manema labarai ta bayyana cewa, ta fahimci mazhabar iyalan gidan amnzon Allah (AS) ba da jimawa ba, kuma ta zo ta ganewa idanunta abin da ake yia wajen wanann ziyara, inda ta kara samun yakini dangane da tafarkin Iamm Hussain (AS) wanda shi ne hakikanin tafarkin manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka.

Ta ce ta yi amfani da wannan damar wajen ziyara a wurare masu tsarki, musamman hubbaren Imam Amirul muminin Ali (AS) da ke birnin najaf, inda a can ma ta ga abubuwa da dama da suka kara mata natsuwa kan cewa hakika sadaukarwar da manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa suka yi sun yi hakan ne domin tabbatar da cewa al'umma ta tsira.

Wanann mata dai tana daga cikin wadanda suka zo daga nahiyar Afirka, kamar yadda kuma akwai wadanda suka zo daga wasu kasashen duniya daban-daban- da hakan ya hada har da kasashen Asia da kuma na turai.

3547378


captcha