IQNA

Tare Da Halartar Ayatollah Araki Da Tawagar Iran:

Zaman taro Kan Wajabcin Hadin Kan Musulmi A Indonesia

22:55 - November 28, 2016
Lambar Labari: 3480982
Babgaren kasa da kasa, a jibi ne za a fara gudanar da taron hadin kan al'ummar musulmi tare da halartar Ayatollah Araki a kasar Indonesia.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar taqrib cewa, taron zai gudana ne a karkashin cibiyar Muhammadiyyah tare da gwiwa da cibiyar kisanto da mazhabaobin muslunci, za a yi taron ne a birnin Jakarta fadar mulkin kasar Indonesia a ranar 30 ga wannan wata na Nuwamba.

Taron zai samu halartar masana da malamai daga kasashen duniya daban-daban musamman ma na asia da suka hada da Phlipines, Burnei, Thailand, Malaysia da sauransu.

Batun hadin akn al'ummar musulmi wanda wajibi daga cikin wajibai na addinai shi en kan gaba a cikin abubuwan da taron zai yi dubia kansu, kamar yadda kuma zai dubi kan batun palastinu, da kuma tsatsauran ra'ayin takfir da ma wasu matsaloli da suke cima musulmi tuwo a kwarya.

Tawagar Iran za ta halarci taron karkashin jagoranci bababn sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci Ayatolah Mohsen Araki.

3549674


captcha