IQNA

Gwamnatin China Na Bin Diddigin Lamarin Alhazan Kasar

23:53 - August 06, 2018
Lambar Labari: 3482867
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar China ta saka wata alama kan katunan ‘alhazan kasar da za su sauke farali a bana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wannan shekara gwamnatin kasar China ta saka wata alama kan katunan ‘alhazan kasar da za su sauke farali.

Wannan mataki na zuwa a ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta China take sanya ido a kan dukkanin harkokin musulmin kasar, bisa hujjar yaki da ta’addanci.

Sai cibiyoyin musulmin kasar ta China da suke kula da lamarin aikin hajji sun bayyana cewa, wannan alama za ta taimaka wajen bayar da karya da tsaro ga dukkanin alhazan kasar da suka tafi Saudiyya.

Da dama daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama suna sukar gwamnatin kasar China kan takurawa musulmin kasar da take yi musamman a baya-bayan nan, inda akan tilasta su yin abin da ya saba wa addininsu.

Haka nan kuma wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na cewa wanann alama da aka saka a kan katunan alhazan kasar China, wata hanya ce ta yin liken asiri a kansu.

3736317

 

 

captcha