Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, nan ba da jimawa ba babbar cibiyar nazarin addinin musulunci ta Iman da ke birnin Vienna na kasar Austria za ta fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan ilmomin musulunci da za a iya bayar da diiri a kansa.
Wannan shiri dai zai kunshi daukar laccoci ne daga kwararun malamai masana kan addinin muslunci, wadanda za su rika gabatar da lacca da kuma bayar da makalolinsu ga mahalarta horon.
Wadanda za su halarci shirin dai dole ne shekarunsu kada su haura arbain, kamar yadda kuma shirin zai dauki lokaci ana gudanar da shi bisa tsarin da aka yi, daga karshe bayan kammala horon zai za a baya da shedar digiri.
Zuwa ranar 31 ga watan Agusta da muke ciki ne za a kammala rijistar dukkanin mutanen da suke bukatar shiga shirin.