IQNA

Masana 450 Ne Za Su Halarci Taron Kualalampour 2019

22:42 - November 22, 2019
Lambar Labari: 3484266
Bangaren kasa da kasa, Matir Muhammad ya ce masana 450 ne za su halarci taron Kuala Lampour na shekarar 2019.

Bangaren kasa da kasa, Mahatir Muhammad firayi ministan Malaysia ya bayyana cewa masana 450 ne za su halarci taron Kualalampour.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a wata zantawa da manema labarai Mahatir Muhammad firayi ministan Malaysia ya bayyana cewa masana daga kasashen za su halarci taron wanda Turkiya da Malysia suka shirya.

Ya ce kasashe wadanda za su bayar da gudunmawa wajen hada taron da suka hada da Turkiya, Pakistan da Qatar da kuma Indonesia, da nufin ganin an samu wata hanya ta samar da fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin kasashen musulmi.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, babbar manufar taron wanda shi ne irinsa na farko da za a gudanar a kasar, ita ce tabbatar da cewa musulmi sun koma kan turnba ta hadin kai.

Taron Kualalampour 2019 zai fara daga ranar 18 ga Disamba zuwa ranar 21 ga wata.

 

3858696

 

 

captcha