IQNA

Cibiyar Azhar Ta Yi Allawadai Da Cin Zarafin Musulunci A Holland

19:34 - December 31, 2019
1
Lambar Labari: 3484362
Masu fada da yada kyamar musuunci a cibiyar Azhar sun yi tir da Geert Wilders mai kyamar musulunci a Holland.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin islamicnews.org.sa ya habarta cewa, masu yaki da akidar nuna kyama ga musulunci na cibiyar Azhar sun fitar da bayani da ke tir da matakan da masu kiyayya da muslunci a Holland suke dauka.

Bayanin ya ce irin wadannan matakai babu abin da suke jawowa in banda fitina a tsakanin al’ummomi, domin kuwa hakan yana a matsayin tsokana ne ga dukkanin musulmi na duniya baki daya.

Haka nan kuma sun bukaci mahukunta a kasar Holland su dauki matakan da suka dace domin taka burki ga masu yunkurin fitar da zane-zanen batunci ga manzon rahma a kasar.

Kamar yadda bayanin ya ce sau tari a kan samu masu satsauran ra’ayi daga dukkanin bangarori na mabiya addinai, wanda uma wasu lokuta ayyukan tsokana kan iya jawo fitina a tsakaninsu, wanda zai iya shafar wadanda ba su ba su gani ba.

Dan majalisar dokokin kasar Holland mai tsananin kiyayya da addinin muslunc, ya shirya gudanar da wata gasa ta zane-zanen batunci a kan manzon Allah (SAW) wadda za a gudanar nan ba da jimawa, lamarin da ke ci gaba da jawo cece ku ce a duniya.

Ko a shekarun baya ma ya taba yin wani makamancin hakan, inda ya rubuta wani littafi mai suna fitina, inda ya wulakanta kur’ani mai tsarki da kuma yin izgilin ga addinin musulunci.

 

https://iqna.ir/fa/news/3867832

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
AMINU SALE KWARE
0
0
YA ALLAH KA TO ZARTA MAI KIN ADDININ MUSULUNCI DUK WANDA YACE AMIN YA ALLAH KA DAUKAKA SHI KAYI MAI RAHAMA KUMA KABASHI NASARA ARAYUWA SHI
captcha