IQNA

Amurka Ta Sanya Sharadin Yanke Alaka Da Hizbullah Kafin Taimaka Ma Gwamnatin Lebanon

23:39 - January 24, 2020
Lambar Labari: 3484445
Jaridar Alakhbar ta bayar da rahoton cewa Mike Pompeo ya bayyana cewa sharadin taimaka ma gwamnatin Lebanon shi ne yanke alaka da Hizbullah.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin jaridar Alakhbar ya sheda cewa, Amurka ta ja sabuwar daga da sabuwar gwamnatin kasar Lebanon.

Rahoton ya ce a zantawarsa da wasu kafofin yada labarai, Mike Pompeo sakataren harkokin wajen Amura ya bayyana cewa, sharadin taimaka ma gwamnatin Lebanon shi ne sauraren bukatun al’ummar kasar Lebanon.

Ya ce zanga-zangar da mutane suke yia  Beirut ita ce neman gwamnati ta yanke alaka da kungiyar Hizbullah, saboda haka wannan bukatar da ya kira ta mutane ita e Amurka tak bukata kafin bayar da duk wani taimako ga gwamnatin Lebanon.

Wannan matakin yana zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar turai suka nuna cikakken goyon bayansu ga sabowar gwamnatin ta Lebanon.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3873694

 

captcha