IQNA

Moroco Na Ci Gaba Kara Fadada Alakarta Da Yahudawan Sahyuniya

23:40 - February 12, 2021
Lambar Labari: 3485644
Tehran (IQNA) A ciki gaba da kara fadada alaka tsakanin gwamnatin Morocco da kuma yahudawan sahyuniya, an cimma matsaya tsakanin bangarorin kan bunkasa harkokin ilimin makarantu a tsakaninsu.

Kafofin yada labarai na gwamnatin kasar Morocco sun bayar da rahotanni da ke cewa, ministan ilimi mai zurfi na kasar Saeed Imzazi, da kuma ministan ilimi na gwamnatin yahudawan Isra’ila, sun cimma matsaya kan yin aiki tare a bangaren harkokin ilimi a tsakaninsu.

Bisa ga wadannan rahotani an gudanar da wannan ganawa ne a jiya Alhamis ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, inda bangarorin biyu suka jaddada cewa sun kudiri aniyar bunkasa alakarsu a bangarori daban-daban da suka shafi ma’aikatunsu.

A cikin watan Disamban da ya gabata ne dai sarkin kasar Morocco Muhammad na shida, ya sanar da kulla alaka tsakanin kasarsa da kuma gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Wannan mataki dai yana zuwa ne sakamakon matsin lamba da Morocco ta fuskanta daga tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump kan yin hakan, tare da yi wa kasar ta Morocco alkawalin cewa Amurka za ta amince da yankin yammacin sahara a matsayin wani bangare na kasar Morocco.

Kafin Morocco dai Trump ya yi irin wannan matsin lamba a kan kasashen hadaddiyar daular larabawa da kuma Bahrain, wadanda su ma ya tilasta su suka kulla hulda ta diflomasiyya da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

3953574

 

captcha