IQNA

Tarukan Tarbar Watan Ramadan A Kasar Habasha

23:40 - April 11, 2021
Lambar Labari: 3485797
Tehran (IQNA) musulmi suna gudanar da tarukan tarbar watan mai alfarma a kasar Habasha.

Shafin al-ain.com ya bayar da rahoton cewa, al’ummar yankin Zabi Maula da ke kudancin kasar Habasha wadanda akasarinsu musulmi ne, suna gudanar da tarukan tarbar watan mai alfarma akowace shekara.

Sheikh Muhammad Amin Sheikh wanda shi ne shugaban cibiyar kur’ani ta yankin Zabi Maula ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na dari da goma sha daya da wannan cibiya take gudanar da tarukan tarbar watan ramadan a kowace shekara.

Wannan cibiya dai ita ce cibiyar kur’ani mafi jimawa  akasar habasha wadda tun daga lokacin da aka gina ta take gudanar da ayyukanta fiye da shekaru dari da suka gabata.

Ya ce babbar manufar gudanar da tarukan tarbar watan ramadan ita ce tunatar da musulmi zagayowar wannan lokaci mai albarka, da kuam zama cikin shirin fara ibadar azumi da sauran ayyukan bautar Allah a cikin wannan wata.

Baya ga haka kuma, a tarukan tarbar watan ramadan da ake yi a wannan cibiya fiye da shekaru dari da goma sha daya, ana gudanar da karatun kur’ani da kuma wa’azi da tunatarwa.

3963737

 

 

 

 

captcha