IQNA

Mahardacin Kur'ani Kuma Mai Wakokin Yabon Manzo

Tehran (IQNA) Fauzi Muhammad Iyad makaracin kur'ani kuma mai wakokin yabon manzon Allah a kasar Masar.

Shafin yada labarai na Sadal Balad ya bayar da rahoton cewa, Fauzi Muhammad Iyad makaracin kur'ani kuma mai wakokin yabon manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi da alayensa tsarkaka, an haife shi ne a cikin shekara ta 1992 a Lardin Buhaira na kasar Masar.

Tun yana karami ya hardace kur'ani mai tsarki, inda a halin yanzu yana daga cikin fitattun makaranta kur'ani a kasar, kamar yadda kuma ya shahara  a fagen wakokin addini da yabon manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi da alayensa tsarkaka.

Yana bin salon rera wakokin addini ne irin na daddun malamai da suka shahara a wannan fage a kasar, irin su sheikh Muhammad Imran, Sayyid Naqshbandi, sheikh Nasruddin Tubar, da makamantansu da suka shahara  a kasar ta Masar a wannan fage.

Fauzi Muhammad Iyad shi ne ya zo na daya  a gasar kur'ani ta Masar a wannan watan ramadan da ya gabata, kamar yadda kuma shi ne ya zo na daya  a gasar kur'ani ta Port Saeed ta kasa da kasa a shekarar 2019.

Ya samu kyautuka na girmamawa a lokuta daban-daban daga cibiyoyin addini a kasar Masar da suka hada da cibiyar azhar.

3983240

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: watan ramadan ، wakokin yabon manzo ، girmamawa ، cibiyar azhar