Shafin yada labarai na sadal balad ya bayar da rahoton cewa, a cikin salon karatu na musamman Sheikh Mahmud Shuhat yana karanta surat Quraish.
Shuhat ya yi karatun kur'ani a gaban mahaifinsa tun yana karami, kafin daga bisani kuma ya shiga makaranta inda ya ci gaba da karatu da kuma mayar da hankalia bangaren ilimin kur'ani.
Ya ce ya yi karatu a jami'ar azhar a bangaren ilmomin addinin muslunci, kamar yadda kuma yana gabatar da karatun kur'ania wuraren taruka.
Haka nan kuma ya kara da cewa, a lokacin mulkin Husni Mubarak ya yi karatu a wuraren taruka tare da halartar Mubarak, da kuam manyan mutane gami da malamai da baki na kasashen ketare.
Haka nan kuma ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya da dama domin gabatar ad karatun kur'ani mai tsarki a wuraren taruka na kur'ani.