IQNA

An Fitar Da Wani Dan Majalisa Daga Zauren Majalisar Saboda Tufafin Musulunci a Zambia

22:06 - December 17, 2021
Lambar Labari: 3486695
Tehran (IQnA) An fitar da wani dan mjalisa musulmi saboda saka tufafin musulunci a kasar Zambia

Jaridar Lusaka Times ta bayar da rahoton cewa, kakakin majalisar dokokin kasar Zambia ya bayyana  cewa tufafin da Munir Zulu, wakilin gundumar Lumzi ya sanya a zaman majalisar ya saba wa ka'ida kan tufafin da ya kamata dan majalisa ya sanya a cr.

Zulu ya bayyana cewa bai taka wata doka da ta saba wa ka'idar sanya tufafi a majalisar ba saboda ana iya amfani da rigar Musulunci a matsayin tufafin gargajiya na Afirka.
 
Saka tufafin irin na musulmi da Munir Zulu ya yi, ya jawo tayar da jijiyoyin wuya a majalisar, tsakanin masu adawa da kuma masu goyon bayansa, amma dai shugaban majalisar ya tsaya kai da fatan a kan cewa dole ne ya fice daga majalisar, har sai ya canja tufafin da ke jikinsa.
 
Zambiya tana kudu masu gabashin Afirka wadda da ke mutane miliyan 18.5, kuma musulmi su ne ke adadi mafi karanci a kasar, idan aka kwatanta da kiristoci da kuma masu bin addinin gargajiya na kasar.
 

4021534

 

captcha