An haifi Dr. Ahmad Mustafa a birnin Alexandria na kasar Masar a shekara ta 1943 kuma kwararre ne, mai bincike kuma kwararre a fannin fasaha da zane na addinin Musulunci.
Asalin iliminsa dai ya karance shi ne a turance wato neoclassical style of graphics design, ya samu kwarin gwiwa sosai daga masu fasahar zane da rubutu na musulunci.
Mustafa ya kammala karatun digirin digirgir a Jami'ar Alexandria a shekarar 1966 sannan ya samu gurbin karatu don ci gaba da karatun digiri a kasar Burtaniya.
Ya kuma halarci darussan horo kan zane-zane na duniya da yawa kuma yana da mujallu na kimiyya da yawa.
Daga nan Mustafa ya gano tushensa na Musulunci, ya kuma gabatar da ayyukansa a cikin tsari na zahiri bisa ayoyin Alkur'ani, kuma ya samu damar yin hakan, sakamakon wata sabuwar hanya ta hada fasaharsa da kuma wani sabon kirkirran salon a fasahar zane wanda shi ne ya kirkiro shi a karon farko.
a matsayinsa na babban mai zane-zane a cikin fasahar rubutun Musulunci, ya zuwa yanzu ya gudanar da ayyuka masu daukar hankula matuka.
Dr. Ahmad Mustafa ya rayu kuma yana aiki a Landan tun 1974, Shi ne daraktan cibiyar ayyukan fasahar Larabawa a Burtaniya, wadda ya kafa a shekarar 1983, kuma ya koyar da a sassa da dama a jami’oi na duniya.