Sheikh Abdulfattah Taruti ya ce, bayan shekaru biyar da rasuwar Fitaccen Makarancin Kur'ani Sheikh Muhammad Al-laithi , mahaifinsa ya rasu, inda bisa ga al'ada a kasar masar a kan bizne iyalan gida guda kabrukansu kusa da juna.
A lokacin gina kabarin mahaifinsa a kusa da kabarinsa, mai aikin ginar kabarin ya tono kabarin Sheikh Muhammad Al-laithi da ke gefe, kuma an ga gawarsa kamar yadda aka bizne shi da gangar jikinsa ba ta yi komai ba, bayan shekaru biyar da rasuwarsa.