IQNA

Karatun Kur'ani Daga Surat Maryam (AS) Tare Da Hani Al-Azzuni

Tehran (IQNA) Hani al-Azzuni, matashin makaranci dan kasar Masar, ya karanta ayoyin farko na surar Maryam (AS) a daya daga cikin bidiyonsa.
Hani Al-Azzuni shahararren makaranci ne daga Mansoura da ke lardin Daqahliyah na kasar Masar, wanda baya ga karatun kur'ani, yana da kyakykyawan tarihin yin wakokin addini da Ibtihal.
 
Saboda da himmarsa wajen karatunsa, ya yi matukar farin jini, musamman a tsakanin matasan Masar, kuma an san shi a matsayin mai salo daban-daban wajen karanta kur'ani mai tsarki.
 
A cikin bidiyon da ke kasa, za ku iya kallon karatun aya ta farko zuwa ta takwas tare da wannan matashi.
Abubuwan Da Ya Shafa: matasan Masar ، musamman ، surat Maryam