IQNA

Dubban Mutane Sun Gudanar Da Taron Tunawa Da Janar Qassem Sulaimani Da Abu Mahdi Muhandis A Iraki

22:07 - January 01, 2022
Lambar Labari: 3486765
Tehran (IQNA) dubun-dubatar al'ummar Iraki ne suka gudanar da gagarumin taro yau a birnin Bagada domin tunawa da shekaru biyu da shahadar Qasem Sulaimani da Abu Mahdi almuhandis.

Miliyoyin mutanen kasar Iraki ne suka fito kan tituna a biranen Bagdaza babban birnin da kuma karbala don tunawa da cikar shekaru biyu da shahadar Janar Kasim Sulaimani babban kwamandan rundunar Kudus ta Jumhuriyar musulunci ta Iran da kuma mataimakin shugaban dakarun Hashdushabi na kasar Iraki Mahdi Almuhandis wadanda suka jagorinci yakar kungiyar ‘yan ta’adda ta Deash a kasar Iraki.
تجمع میلیونی بغداد به مناسبت سالگرد شهادت سردار سلیمانی:خون‌بهای این شهدا خروج کامل نظامیان اشغالگر است
 
Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya ce tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ne ya bada umurnin kashe Janar Sulaimani a kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Bagdaza a ranar 3 ga watan Jenerun shekara ta dubu biyu da ashirin.
تجمع میلیونی بغداد به مناسبت سالگرد شهادت سردار سلیمانی:خون‌بهای این شهدا خروج کامل نظامیان اشغالگر است
 
Amma kwanaki biyu bayan haka majalisar dokokin kasar Iraki ta amince da kodurin korar dukkan sojojin kasashen waje daga cikin har da na AMurka daga kasar, bayan kissan. Wannan dokar ta tilastawa sojojin Amurka barin kasar Iraki zuwa karshen shekara ta 2021 da ta gabata.
تجمع میلیونی بغداد به مناسبت سالگرد شهادت سردار سلیمانی:خون‌بهای این شهدا خروج کامل نظامیان اشغالگر است
 
Banda haka mutanen masu juyayin shahadar kwamandojin yakar Daesh a kasar ta Iraki sun konan tutocin Amurka da Isra’ila a kusa da yankin da ifisoshin jakadadancin kasashen waje suke a birnin Bagdaza.
تجمع میلیونی بغداد به مناسبت سالگرد شهادت سردار سلیمانی:خون‌بهای این شهدا خروج کامل نظامیان اشغالگر است
 
Mutane da dama sun yi allawadai da kisan shahid Sulaimani, daga cikin har da wasu ‘yan siyasa a kasar ta Amurka. Shugaban dakarun Hashdushaabi na kasar ta Iraki ne Fali Fayyad ya yi jawabin bayan gangamin na tunawa da wadannan shahidai.
 

 

 

 

captcha