Lailatul Qadr ( ko daren lailatul kadari) yana nufin daren daraja, A cikin wannan dare ne farkon wahayin Ubangiji ya sauka a cikin zuciyar Manzon Allah (SAW). sauka ta bai daya, amma sauaka ta mataki-mataki ta zo ne a cikin tsawon shekarun manzanci na manzon Allah (SAW).