An gudanar da taron iyaye mata da jariransu don tunawa da jariri dan Imam Husaini (AS) dan watanni 6, Ali Asghar (AS), wanda aka kashe ba tare da jin kai ba a yakin da aka kaddamar kan zuriyar manzon Allah (SAW) a Karbala a shekarar ta 61 hijira Kamariya, 680 bayan haihuwar Annabi Isa.