IQNA

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a harin da Isra'ila ta kai a Rafah

IQNA - Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kaddamar da farmaki ta sama kan wani sansani da ke karbar 'yan gudun hijirar Palasdinawa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza a ranar 26 ga watan Mayun 2024. Akalla mutane 40 da suka hada da mata da kananan yara ne suka yi shahada a harin tare da jikkata wasu da dama.