'Yan Kashmir sun yi Allah wadai da harin da yahudawan sahyuniya suka kai wa Iran
IQNA- Al'ummar Srinagar na yankin Kashmir sun fito kan tituna a ranar 14 ga watan Yunin 2025, suna yin kakkausar suka kan wannan mummunan harin da yahudawan sahyuniya suka kai wa Iran. Sun yi ta rera taken nuna adawa da gwamnatin Isra'ila da Amurka.