IQNA

Ana Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Ta Kasa A Nigeria

21:15 - February 20, 2014
Lambar Labari: 1377677
Bangaren kasa da kasa, Ana ci gaba da gudanar da gasar karatun kur'ani da kuma harda a mataki na kasa a tarayyar Nigeria da ke gudana a garin Dutse fadar mulkin jahar Jigawa da ke arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na All Africa cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da gasar karatun kur'ani da kuma harda a mataki na kasa a tarayyar Nigeria da ke gudana a garin Dutse fadar mulkin jahar Jigawa tare da halartar makaranta da mahardata daga wasu sassa na kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, mataimakin shugaban Nigeria Namadi Sambo ya yi bayani dangane da wannan gasa da take gudana yanzu haka a jahar ta Jigawa, inda ya ce babbar manufar gudanar da irin wannan gasa ita ce kara kiyayaye koyarwa irin ta addinin muslunci a tsakanin al'ummar musulmi na kasar, wanda kuma koyarwar kur'ani ita hakikanin koyarwar da musulmi zai bi domin aiwatar da addinin kamar yadda Allah yake uamrtarsa.

Ya kara da cewa ya zama wajibi kan malaman addinin muslunci ta su taka gagarumar rawa wajen kara wayar da kan mutane dangane da muhimamncin wannan gasa, wadda za ta taimaka ma matasa wajen rungumar karatu da harder kur'ani a kasar, ya ce a kowane lokaci za su ci gaba da karfafa gwiwar gudanar da irin wannan gasa tare da bayar da dukkanin taimakon da hakan ke bukata.

Nigeria dai na daga cikin kasashen Afirka da suke taka gagarumar rawa ta wanann fuska a mataki na nahiyar Afirka da ma na kasa da kasa, kamar yadda takan dauki matsayi na daya a wasu lokutan da ake gudanar da gasar kur'ani ta duniya.

1376629
 

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
captcha