IQNA

Al'ummar Gaza Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Musulmin Afirka Ta Tsakiya

18:10 - February 24, 2014
Lambar Labari: 1379467
Bangaren kasa da kasa, daruruwan mutane sun gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya ga al'ummar jamhuriyar Afirka ta tsakiya sakamakon kisan kiyashin da mabiya addinin kirista suke yi a kansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Ma'an cewa, a jiya daruruwan mutane sun gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya ga al'ummar jamhuriyar Afirka ta tsakiya sakamakon kisan kiyashin da mabiya addinin kirista suke yi a kansu ba tare da kakkautawa ba.

A nata bangaren babbar jami’ar hukumar kare hakkokin bil’adama ta MDD Navi Pillay ta bayyana cewar musulman kasar Afirka ta tsakiya suna ci gaba da fuskantar hare-hare daga wajen ‘yan daban Anti-Balaka na kasar don haka ta kirayi sabuwar gwamnatin kasar da ta kara kaimi wajen kawo karshen wannan rikicin.
Navi Pillay ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din nan Litinin inda ta ce lamarin tsaro da kare hakkokin bil’adama na ci gaba da tabarbarewa a kasar Afirka ta tsakiyan cikin ‘yan kwanakin baya-bayan nan inda ake ci gaba da korar musulmin.
Jami’ar ta ci gaba da cewa kisan gillan da ake yi wa musulmin ya zamanto ruwan dare , don haka ta kirayi kasashen duniya da su yi wani abu wajen kawo karshen irin wannan zubar da jinin.
Ita ma a nata bangaren kungiyar Amnesty International mai fafutukan kare hakkokin bil’adama ta sanar da cewa dakarun kasa da kasa masu tabbatar da zaman lafiya a kasar sun gaza wajen kare musulmin daga hare-haren da ake kai musu.

1378504

Abubuwan Da Ya Shafa: gaza afirka
captcha