IQNA

Addinin Musulunci Ya Barranta Daga Akidar Takfiriyyah

21:50 - March 04, 2014
Lambar Labari: 1383072
Bangaren kasa da kasa, wani daya daga cikin malaman addinin muslunci a cibiyar Azahar da ke kasar masar ya bayyana akidar kafirta musulmi da ta sake bayyana a matsayin babban bala'I da ya bulla a cikin musulmi tare da cewa musulunci ya barranta daga wannan akida.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto, daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin malaman addinin muslunci a cibiyar Azahar da ke kasar masar Muhammad Abdul-ati ya bayyana akidar kafirta musulmi da ta sake bayyana a matsayin babban bala'I a cikin musulmi duk da cewa wannan akida bat a cikin addinin musulunci.
Malamin ya ci gaba da cewa tun kafin wannan lokacin al'ummar musulmi suna cikin rayuwa duk da banbanci na fahimta ko na mazhaba amma dai suna kallon junansu a matsayin 'yan uwa daya masu addinin guda, wanda Kalmar shahada ta hada su a kan imani da Allah da manzonsa, da kuma littafinsa da alkibla guda daya, amma bayyanar akidar takfiriyyah ta sanya wasu das ka rudu sun fita daga wannan sahu na haduwar al'ummar musulmi a wuri guda, tare da kafirta duk wanda ba su ba.
Malamin ya yi kira ga dukkanin malaman addinin muslunci masu 'yancin lamiri das u safke nauyin day a rataya a kansu, domin fuskantar wannan babbar musuiba da kunno kai a cikin wannan al'umma.
1382106

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha