IQNA

Masar Ta Kori Masu Kare Hakkokin Palastinu Da ke Kokarin Shiga Gaza

19:51 - March 10, 2014
Lambar Labari: 1385549
Bangaren kasa da kasa, mahukunta a kasar asar sun kori wasu masu rajin kare hakkin bil adama da suke kokarin shiga yankin Zrin Gaza da nufin kai goyon bayansu ga al'ummar yankin da suke fuskantar zalunci da killacewa daga haramtacciyar kasar Isra;ila.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na safirnews cewa, a cikin wannan mako mahukunta a kasar asar sun kori wasu masu rajin kare hakkin bil adama da suke kokarin shiga yankin Zrin Gaza da nufin kai goyon bayansu ga al'ummar yankin da suke fuskantar zalunci da killacewa daga haramtacciyar kasar Isra'ila tun tsawon shekaru.

Wadannan mutane sun fito ne daga kasashe daban-daban, da suka hada da na musulmi daga yankin gabas ta tsakiya da kuma Turkiya, kamar yadda tawagar ta kunshi wasu daga kasashen yammacin turai har ma da Amurka, lamarin da yake ci gaba da fuskantar kakakusar suka da yin Allawadai daga kungiyoyin jin kai da na kare hakkin bil adama na duniya.

Kasar Masar dai tana daukar wasu matakai da suke bayar da mamaki a cikin lokutan nan wajen takura ma al'ummar yankin Gaza da suke karkashin zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila, da hakan ya hada da hana shigar musu da taimako da kuma rufe ramukan da ake yin amfani da su wajen shigar da kayayyaki cikin yankin daga kasar masar, kasantuwar haramtacciyar kasar yahudawa bat a bari a shiga da kaya a yankin, duk hakan bisa hujjar cewa Hamas na yin shigar shugula a cikin ahrkokinsu.

1384594

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha