
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, kungiyar tarayyar Afirka ta saka kungiyar kiristoci ‘yan ta’adda da ake kira anti balaka a kasar Afirka ta tsakiya a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda bayan da kungiyar ta dauki matakin kai hare-hare kan musulmi ba dare ba rana, lamarin da ya tilasta su gudun hijira.
Dakarun kiristoci na Anti-Balaka na Africa ta Tsakiya sun toshe hanyar shiga kasar Camaroo daga kasar wanda musulmi masu tserewa daga kasar suke bi, majiyar hukumar yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya ce ta bayyana haka a jiya jumma’a ta kuma kara da cewa.
Melissa Fleming, kakakin hukumar ya kara da cewa, toshe hanyar ya sanya wasu musulman suka koma baya suka kama wata hanya wanda zai dauke su wasu watanni 2-3 kafin su isa arewa maso gabacin camaroo.
Fleming, ta kara da cewa musulmin sun taka da kafa na watanni biyu kafin su isa inda aka hanasu wucewa. Sannan a cikin tafiyar tasu, suna tafiya cikin dare ne su boye da rana don kada a gano su. A abinci kuma sukan ci ganye da yayan itatuwa da kuma ruwa masa kyau.
1395189