IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Mai Tsarki A Iran

16:50 - May 28, 2014
Lambar Labari: 1411964
Bangaren kasa da kasa, an bude babbar gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Tehran tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya kimanin 70.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a yau an bude babbar gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Tehran tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya kimanin saba'in wafanda za su kara da juna.

An bude gasar ne tare dahalartar alkalin alkalai na asar Iran wanda kuma shi ne mutum na uku a tsarin shugabancin kasar Iran, wanda ya gabatar da jawabi dangane da matsayin gasar da kuma muhimmancinta  wajen karfafa gwiwar makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki a kasashen musulmi.

A yayin gudanar da gasar dai za a fitar da matsayi na daya da na biyu da kuma na uku a dukkanin bangarorin gasar, wanda hakan ya hada da bangaren karatu a dukkanin bangarorin kur'ani daga farko har zuwa karshe, haka nan kuma akwai bangaren juzu'ai, sai kuma bangaren harda, wanda shi ma matakai ne kamar dai bangaren karatu, akwai na dukkanin ku'ani kuma akwai na bangarori.

1410830

Abubuwan Da Ya Shafa: gasa
captcha