IQNA

Na Yi Farin Ciki Da Kasantuwata Makarancin Kur’ani Mai Tsarki

19:05 - June 02, 2014
Lambar Labari: 1413798
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin makaranta kur’ani mai tsarki da ya halarci wannan gasa da aka gudanar karo na talatin da daya a kasar Iran daga kasar Uganda ya nuna matukar farin cikinsa dangane da yadda rayuwarsa ta kasance a cikin karatun wannan littafi mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shi da Abdulbasit Muhammad Abdi daya daga cikin makaranta kur’ani mai tsarki da ya halarci wannan gasa da aka gudanar karo na talatin da daya a kasar Iran daga kasar Uganda ya nuna matukar farin cikinsa dangane da yadda rayuwarsa ta kasance a cikin karatun wannan littafi mai tsarki wanda Allah madaukakin sarki ya sany6a ya zama hanyar shiriya ga talikai.
Makarancin ya nuna gamsuwarsa da yadda wannan gasa ta gudana a birnin Tehran tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya daban-daban, wanda hakan ya kara tabbatar wa duniya cewa a kowane lokaci kur’ani littafi ne rayayye, wanda yake a cikin zukatan mabiya addinin muslunci kuma yake ci gaba da kasancewa kundin tsarin rayuwarsu.
A yau ne dai ake kamala gasar a birnin Tehran, wanda hakan shi ne karo na 31 da ake gudanar da wannan gasa, kuma tana daya daga cikin irinta na duniya da ake gudanarwa da ke samun halartar makaranta da mahardata daga kasashe fiye da saba’in na duniya.
1412334

Abubuwan Da Ya Shafa: uganda
captcha