IQNA

An Dakatar Da Kakakin Kungiyar Makaranta Kur’ani Na Kasar Masar

23:55 - June 24, 2014
Lambar Labari: 1422187
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan Masar sun dakatar da wani malamin addinin musulunci kuma makarancin kur’ani kuma kakakin gamayyar makarnata da mahardata akasar, saboda ya bayar da labara dangane da yadda wasu makaranta suka yi karatu da salon kiran sallah na mabiya tafarkin iyala gidan manzo.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a ci gaba da daukar munanan matakai da mahukuntan Masar suke yi kan masu bin tafarkin Ahlul bait sun dakatar da wani malamin addinin musulunci kuma makarancin kur’ani kuma kakakin gamayyar makarnata da mahardata akasar, saboda ya bayar da labara dangane da yadda wasu makaranta suka yi karatu da salon kiran sallah na mabiya tafarkin iyala gidan manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka. A wani labarin kuma wata kungiya farar hula mai fafukar 'yanci alkalai a kasashen larabawa ta yi a…wadai dangane da yadda kotu ke yanke hukuncin kisa a kasar sannan ta bukaci Alkalan na Masar da su dakatar da yanke hukuncin kisa a kasar ta Masar. Kungiyar ta ce tun bayan juyin milki a kasar Masar ta masar tsahon shekaru guda kacal an yankewa Mutane 1264, idan aka kwatamta da shekarun baya adadin Mutane da aka yankewa hukuncin kisan ya linkin balinke.inda a shekara ta 2009 Mutane 136 aka yankewa hukuncin kisa a kasar ta Masar sai kuma shekaru na 2010 da 2011 inda aka yankewa Mutane 134 da kuma 115 hukuncin kisa a kasar. Kungiyar ta ce kotun kasar Masar ta huce gona da iri wajen yanke hukuncin kisa a tsahon wannan shekara domin hukuncin da ake yanke wa ba shi da wata alaka dangane da wanda ake tuhumar. A watanin baya-bayan nan dai kotun Masar ta yankewa magoya bayan 'yan uwa musulmi da dama hukuncin kisa inda a hukuncin baya-bayan nan aka yanke hukuncin kisan kan Mutane 183 daga ciki kwa hard a shugaban kungiyar Muhamad Badi'i. 1420832

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha