IQNA

Shugaban Kasar Iran Ya taya Al'ummar Musulmi Murnar Shiga Watan Ramadan

20:09 - June 29, 2014
Lambar Labari: 1423899
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Iran Sheikh Hassan rauhani ya taya al'ummar musulmin duniya murnar shiga watan ramdan mai alfarma tare da yi musu fatan alkahiari da kuma addu'ar Allah ya karbi ibadunsu a cikin wanan wata mai albarka.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, al'umma a jamhuriya musulinci ta Iran zasu dauki azumi Lahadi idan Allah ya kai bayan an hango jinjirin watan na Ramalana dazu a wasu sassan kasar.   Hango jijinrin watan na a matsayin ranar karshe ta watan Sha’aban sannan kuma gobe Lahadi a matsayin ranar farko na watan Ramalana na wannan shekara ta 1435. 

Dama tunda farko kasashen da dama sun sanar da daukan azumin a gobe lahadi idan Allah ya kai mu. A tarayya Najeriya dai yau al'umma musulmai sun wuni da Azumin farko bayan sanarda sinkayen jinjirin watan jiyya, koda yake wasu rahotanni sun ce jama'a da dama basu daukin azumin ba a yau, saboda basu ji sanarwar fara azumin ba.

Daga cikin kasashen da suka sanar da ranar Lahadi a matsayin ranar farko ta watan Ramadan, akwai Iran, Sadiyyah, Masar, Palastinu, Jordan, Iraki, Somalia, Syria, Indonesia da kuma Malazia, yayin da wasu kasashen kuma da suka sanar da ganin wata a ranar Juma'a suka tashi da azumi a jiya Asabar, daga ciki kuwa har da kasashen Yemen, Turkiya da kuma Najeriya.
1423283

Abubuwan Da Ya Shafa: rauhani
captcha