IQNA

An Girmama Babban Malamin Azhar A Gasar Kur'ani Ta Dubai

13:09 - July 03, 2014
Lambar Labari: 1425377
Bangaren kasa da kasa, a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanr a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa an girmama babban malamin Azahar a matsayin babban mutum na duniya musulmi na wannan shekara.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-bayan cewa, a jiya gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanr a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa an girmama babban malamin Azahar a matsayin babban mutum na duniya musulmi na wannan shekara da muke ciki, kamar dai yadda bayanin ya sanar.
Sai kuma a wani bangaren sheikhun Azhar na kasar Masar ya nuna damuwarsa dangane da samuwar masu akidar kafirta musulmi a wasu kasashen larabawa da na musulmi.  Kanfanin dillancin labarai na kasar Iran ya habarta cewa a yau assabar Sheikh Ahmad Tayyib na jami'ar Al'azhar ta kasar Masar ya bayyana a tashar telbijin ta kasar inda ya bayyana damuwarsa dangane da samuwar akidar kafirta musulmi a wasu kasashen larabawa da na musulmi.

Ya ce inda yace masu wannan akida sun eke  badda matasa musulmi kuma sun fi makiya musulinci hadari saboda sune suka bayar da fatuwa na kashe Al'ummar musulmi da sunan musulinci kamar yadda yake faruwa a kasashen Siriya,Iraki, Lobnon da kuma abinda yake faruwa yanzu haka a kasar Masar
Sheikh Azhar yace masu irin wannan akida sune suka bada fatawar halarta jinin jami'an 'yan sanda da na Sojoji a kasar ta Masar kuma suke baiwa Al'ummar kasar  umarni fito na fito da hukumomi a kasar
Kafin wannan bayanai, an kara fadada kai hare hare kan dakarun tsaron kasar Masar daga kungiyoyin masu dauke da makamai tare da wasu mayaka masu alaka da kunigyar Ansaru baitul mukkadas a yankin tsibirin Sina bayan samun umarni daga Ayman Zawahiri shugaban kungiyar Alka'ida na kasar ta Masar.
1424553

Abubuwan Da Ya Shafa: Shehul Azhar
captcha