Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, kwamitin tsaron ya fara gudanar da zaman ne bayan kiran da kasar Jordan ta yi kan hakan wadda mamba ce a kwamitin, kuma hakan ya zo ne 'yan sa'oi bayan kiran da shugaban Palastinawa Mahmud Abbas ya yi ne a cikin wani jawabi da ya gatar wanda gidajen talabijin da dama suka nuna shi kai tsaye, inda ya ce duk da cewa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya nuna gazawa wajen kare al'ummar Gaza, amma kuma duk da hakan dole ne ya safke nauyin da ya rataya a kansa kan wannan lamarin. Ko a ranar Juma'ar da ta gabata dai sai kwamitin tsaron ya gudanar da wani zama kan sha'anin na Gaza, amma ya kasa cimma wata matsaya kan matakin da zai dauka, sakamakon nuna goyon baya da Amurka take yi kai tsaye da dukkanin matakan da Haramtacciyar kasar Isra'ila take dauka kan al'ummar Gaza, tare da bayyana hakan da cewa mataki ne na kare kai. Mai magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza Asharaf Qudrah ya bayyana cewa, ya zuwa safiyar yau alkalumman wadanda suka yi shahada ya kai dari shida da hamsin kuma adadin na ci gaba da karuwa, bisa la’akari da yadda sojojin Isra’ila suke ta kara zafafa hare-haren nasu a kan yankuna na fararen hula a daukacin yankin Zirin Gaza.