Kamfamfanin dillancin labaran Iqna a sashen Afirka ya habarta cewa, a cikin wannan makon ne makaranta kur'ani da kuma mahardata Iraniyawa suka gudanar da wani shiri na karatu a gaban wani taro da suka shirya da ya kunshi jakadun kasashen musulmi da ke kasar Uganda kamar dai yadda ake gudanarwa a shekaru baya.
A lokacin bude wannan shiri na karatun kur'ani daya daga ciin fitattun malaman jami'ar Uganda Professor Abidi shi ne ya fara gabatar da jawabinsa, kafin daga bisani wasu daga cikin mahalrta taron da aka gayyata su tofa albarkacin bakinsu, inda ya yaba matuka da irin kokarin da ake gudanarwa wajne ciyar harkar karatun kur'ani mai tsarki a gaba, bisa jagoranci na jamhuriyar musulunci ta Iran.
A bangare guda kuma wasu daga cikin malaman jami'ar Almustafa sun gabatar da jawabi a wurin, inda suka bayyana wannan shiri da cewa babban ci gaban ne aka samu ta hanyar bunkasa karatu da harder kur'ani mai tsarki a cikin kasashen musulmi.
1433490