IQNA

Ana Shirin Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani A Bangaladash

23:53 - August 03, 2014
Lambar Labari: 1435546
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar wata gasar karatu da harder kur'ani mai tsarkia asar Bangadalashe da aka saba gudanarwa a kowace shekara.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na my.we cewa, yanzu haka ana shirin gudanar wata gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki a kasar Bangadalashe da aka saba gudanarwa a kowace shekara a daidai irin wanann lokaci.

Gasar dai za ta samu halartar makaranta da mahardata daga sasa na kasa da kuma wasu daga cikin kasashen yanin, kuma za a gudanbar da ita ne tsawon mako guda, inda za a fitar da matsayi na daya da na biyu da na uku daga dukaknin bangarorin da za a gudanar da gasar, na harda da kuma karatu,da dukkanin bangarorinsa, haka nan kuma bangaren kyautata sauti da kaidojin karatu.

Wanann dai shi karo na goma sha bakawai da ake gudanar da wanann gasa a kasar Bangaladash, kuma tana samun karbuwa daga dukaknin bangarori na musulmin kasar.

1434557

Abubuwan Da Ya Shafa: gasa
captcha