IQNA

Tattaunawa A Birnin Alkahira Na Masar Kan Makomar Rikicin Gaza

17:25 - August 19, 2014
Lambar Labari: 1441110
Bangaren kasa da kasa, bangarorin Palastinawa da ke tattaunawa da ba ta kai tsaye ba tare da bangaren Isra’ila a birnin Alkahira na kasar Masar sun cimma matsaya kan sabunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta har tsawon sa’oi 24.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, wasu majiyoyi a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar sun sheda cewa, tawagar palastinawa ta amince da shawarwarin da gwamnatin Masar ta gabatar dangane da batun dakatar da bude wuta da din-din-din, kuma adaren jiya an mika takardar ga wakilan Isra’ila domin su yi nazari kan shawarwarin.
Daga cikin abin da takardar ta kunsa dai akwai batun dakatar da bude wuta daga bangarorin biyu, kawo karshen killace zirin Gaza, bude dukkanin mashigu a yankin, shigar da kayayyakin abinci da na gine-gine domin sake gina gine-ginen da aka rusa a lokacin yaki tare da sanya ido na majalisar dinkin duniya da gwamnatin palastinawa.
Daga cikin batutuwan da takaddar ta kunsa kuwa har da kara wa palastinawa fadin wuraren da za su yi kamun kifi a cikin ruwa, sai kuma batun palastinawa fursunonin yaki da Isra’ila take tsare da su, wanda za a tattauna batun a wata mai zuwa.
1440494

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha