Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da wani taro an nuna wani babban littafin tafsirin kur'ani mai tsarkia kasar Tunisia a cikin shafula 2197 tare da halatar jami'ai daga bangaren ma'aikatar kula da ayyukan kur'ani mai tsarki wanda ya rubuta wannan tafsiri shi ne marigayi sheikh Sadiq Bilkhair Alyasari.
An dai haifi Sheikh Sadiq Bilkhair Alyasari ne a cikin shekara ta 1918 kuma y rasua cikin shekara ta 2000, bayan ya gudanar da ayyukan masu babban matsayi da kima a banagaren kur'ani mai tsarki da kuma tafsiri, wanda har yanzu ake ci gaba da amfana a das u a cikin kasashen muslmi da ma na duniya baki daya.
Malamin ya rubuta tafsirin kur'ani mai tsarkia cikin shekara ta 1941 mai suna Jami'aul A'azam, kuma har yanzu ana amfani das hi a ajami'oin kasashen larabawa da kuma na musulmi a bangaren karatun ilmomin kur'ani.