Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-magrib Yaum cewa, a jiya an gudanar da wani bababn taro a birnin Tunis na kasar Tunisia mai taken koyar kur'ani da kuma sunnar manzo gami da gajiyarwarsu tare da halartar masana da malamai daga assa na kasar da kuma kasashen ketare.
Abdullah Mosleh shi ne shugaban babbar cibiyar da ke kula da harkokin addini da yada bayanai da suka danganci koyarwar muslunci, ya kuma gabatar da jawabinda a wurin taron inda ya yi ishara da irin muhimmancin da ke tattare da yada oyarwar addinin muslunci a duniya domin isar da sakon da ke tatatre da wannan koyarwar mai albarka.
Ya kara da cewa da dama daga cikin mutanen da ba su san addinin muslunci ba suna kallonsa a matsayin addini da ya kebanta da akida kawai, alhali kuwa musulunci ya hada dukkanin bangarori na rayuwar bil adama da kuma abubuwan da yake bukata a cikin zamantakewarsa da siyasarsa da kuma gudanar da sha'anin mulkinsa.
Wasu na amfani da sunan muslunci wajen bata sunansa aidon duniya, wanda kuma hakan ya yi mummunan tasiri musamman ga al'ummomin da suke rayuwa a kasashen yamamcin duniya.