IQNA

An Tarjama Kur'ani Mai Tsarki Da Yaruka 63 A Birnin Madina

23:43 - September 01, 2014
Lambar Labari: 1445633
Bangaren kasa da kasa, bababr cibiyar da ke kula da ayyuykan tarjamar kur'ani mai tsarkia birnin Madina ta sanar cewa an tarjama kur'ani zuwa harsuna 63 kuma ana shirin yin wata tarjamara cikin harsunan Japan da kuma Ibrananci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-arab da ake bugawa a birnin London na kasar Birtaniya cewa, cibiyar da ke kula da ayyuykan tarjamar kur'ani mai tsarkia  birnin Madina ta sanar cewa an tarjama kur'ani zuwa harsuna 63 kuma ana shirin yin wata tarjamar a  cikin harsunan Japan da kuma Ibrananci nan ba da jimawa ba domin amfanin masu fahimtar wadannan harsuna.
Wannan yana zuwa ne a lokacin da mahukuntan Saudiyya suke kokarin rushe abin da ya saura na tarihin musulunci a birnin makka da madina. Jaridar al-akhbar da ake bugawa a kasar Lebanon ta dauki wani labara a jiya laraba da ke cewa; mahukuntan Saudiyya din da su ka fake da batun fadada masallacin harami da kuma masallacin ma'aiki da ke nmadina, za su rusa tsoffin masallatai masu tarihi.

Daga cikin wuraren da mahukuntan saudiyya din ke shirin rushewa da akwai kabarin manzon Allah da fita da shi daga cikin masalacinsa. Tun a cikin shekarar 1dubu da dari tara da ashirin da hudu ne da zuriyar ali-Sa'uda su ka hau kan karagar mulki ne su ka fara rushe wuraren tarihin musulunci. Kawo ya zuwa yanzu kaso casein da biyar na wuraren tarihin musulunci da ke makka da madina, an rushe su.

1444765

Abubuwan Da Ya Shafa: madina
captcha