IQNA

Horo Ga Limaman Masallatai Kan Ilimin Kur’ani Mai Tsarki A Masar

13:52 - September 03, 2014
Lambar Labari: 1446415
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shiri na horar da malaman addinin muslunci musamamn limaman masallatai da suke jagorantar salloli a masallatai a kasar Masar dangane da ilimin kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Misral Yaum cewa, yanzu haka ana  gudanar da wani shiri na horar da malaman addinin muslunci musamamn limaman masallatai da suke jagorantar salloli a masallatai a kasar Masar dangane da ilimin kur’ani mai tsarki a bangaren gajiyarwa ta littafin mai tsarki da ta gagari mahlukai baki daya.
A wani labarin kuma gwamnatin kasar Masar ta gabatar da wasu sabbin shawarwari dangane da batun dakatar da bude wuta a gaza da kuma bayar da damar shigar da kayayyakin agaji ga al'ummar yankin.
Wasu majiyoyi a cikin tawagar da ke gudanar da tatatunawa kan batun dakatar da bude sun sheda cewa, gwamnatin Masar ta shirya shawarwarin nata ne da suka kunshi bayar da dama a shigar da kayayyakin agaji da magunguna ga al'ummar gaza gami da kayayyakin gine-gine ba tare da bata lokaci ba, tare da jinkirta batun fursunonin palastinawa zuwa da kuma batun bude filin safka da tashin jiragen sama da gabar ruwa zuwa wata guda a nan gaba.
Majiyoyin suka bangaren alastinawan zai iya amincewa da wannan shawara, amma babu tababcin ko bangaren Isra'ila zai amince da hakan, domin kuwa an sha cimma yarjeniyoyi tare da su suna sabawa.
1445199

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha