Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum Sabi cewa, wasu daga cikin manyan malaman babbar cibiyar addinin muslunci ta Azahar sun mayar da kakkausan martini dangane da yunkurin da shugabannin wahabiyawan Saudiyyah suke ni na dauke kabarin manzon Allah daga cikin masallacinsa mai alfarma da ke birnin Madina zuwa makabartar Baki’a.
Malaman wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu ta kafofi daban-daban sun mayar da hankali ne kan irin munin da ke tattare da daukar wannan mataki da mahukuntan na Saudiyya suke da niyyar yi, wanda ya yi hannun riga da addinin muslunci baki daya, kamar yadda ya sabawa dabia ta kyawawan dabiu, domin yin hakan tamkar muzantawa ne gas hi kansa manzon Allah da kuma addinin muslunci.
A cikin wannan makon ne wata jaridar kasar Birtaniya ta buga wani rahoton sirri wanda ke tabbatar da cewa mahukuntan wahabiyawan Saudiyya na da shirin rusa kabarin manzon Allah saboda abin da suka kira shirka da musulmi suke yi a kabarin nasa mai daraja dake cikin masallacin, kuma suna shirin kwashe shi zuwa makabarta.
1446251