IQNA

Taimakon Ayyukan Ta’addanci Haram Ne A Shar’ance

17:14 - September 04, 2014
Lambar Labari: 1446689
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Masar ya bayyana cewa taimaka ma ‘yan ta’adda haramun ne a shar’ance a addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-misriyun cewa, Sheikh Sauki Ibrahim Abdulkarim babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Masar ya bayyana cewa taimaka ma ‘yan ta’adda haramun ne a shar’ance, kuma duk wanda ya yi hakan ya aikata aiki ne na haram.
Wannan fatawa ta zo a daidai lokacin da rahotanni ke cewa an kai hari akan bututun iskar gas a yankin Sina da ke kasar, rahotannin da su ke fitowa daga kasar ta Masar sun ce da safiyar yau alhamis ne wasu mutane da ba a kai ga tantance su ba, su ka kai hari akan bututun da ke daukar Iskar Gaza a garin al-arish da ke arewa da yankin Sinaa.
Shedun ganin ido sun ce harin ya yi sanadin fashewar bututun sannan kuma da tashin gobara. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake kai wa bututun iskar Gas a  da ke isa h.k. Isra’ila da kuma Jordan, a yankin na Sinaa hari a kasar Masar. Yankin na Sinaa na cike da kungiyoyin da su ke dauke da makamai wadanda su ke fada da gwamnatin kasar ta Masar.  
1446183

Abubuwan Da Ya Shafa: shauki
captcha