Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Maa cewa kotun haramtacciyar kasar Isra'ila ta daure wasu palastinawa biyu bisa hujjar cewa sun gudanar da wani shiri na horar da wasu karatun kur'ani mai tsarki wanda a cewar kotun hakan ya sabawa dokokin gwamnatin yahudawan sahyuniya.
Shugaban kwamitin kula da iyalan fursunonin palastinawa da ke gidajen kurkukun Isra'ila a birnin Qods Amjad Abu Asab ya bayyana cewa, sojin yahudawa sun kame Ubrahim Barakah da shekaru 39 da kuma Haisam Ragib Muhammad Ragib dan shekaru 32 da haihuwa, kuma sun tsare sun a tsawon watanni 10, kafin daga bisani su yanke musu hukunci daurin watanni 20 a gidan kaso.
Wannan dais hi ne karo na farko da haramtacciyar kasar Isra'ila take daukar irin wadannan matakai na wariya da takura ga al'ummar palastinu mazauna yankunan gabacin birnin Qods ba, hakan ya zama abin da aka saba das hi a tsakanin al'ummar palalstinawa marassa kariya.
1449443