IQNA

Tarjamar Kur’ani Mai Tsarki A Cikin Yaruka 50 A kadar India

13:11 - September 16, 2014
Lambar Labari: 1450729
Bangaren kasa da kasa, cibiyar da ke kula da ayyukan buga kur’ani da kuma raba a tsakanin mabiya addinin muslunci a kasar India ta kudiri aniyar gudanar da aikin tarjama da kuma buga kwafin kur’anai da yaruka 50 na duniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nan a Magrib Alyaum cewa, shugaban cibiyar da ke kula da ayyukan buga kur’ani da kuma raba a tsakanin mabiya addinin muslunci a India Fadhl Al-karim ya bayyana cewa, sun kudiri aniyar gudanar da aikin tarjamawa da kuma buga kwafi-kwafin kur’anai da yaruka 50 na duniya domin raba a su a cikin kasar dama sauran sassa na duniya.
Ya ci gaba da cewa wannan yana daga cikin manufar kafar cibiyar yada dukkanin wani abu da ya shafi kur’ani da koyarwa ga musulmin kasar da kuma isar da hakan ga sauran wadanda ba musulmi ba a kasar da ma kasashen ketare.
Fadhl Karim ya gana da shugaban kungiyar kasashen musulmi Abdulmuhsin Turki a kasar Saudiyya dangane da wannan batu, da kuma irin gudunmawar da kungiyar kasashen musulmi za ta bayar domin ganin wannan aiki ya tabbata kuma  an aiwatar da shi cikin nasara.
1449937

Abubuwan Da Ya Shafa: india
captcha