Kamdanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ma’a daga yankin palastinu cewa, a jiya an gudanar da wani zaman muhawara tsakanin manyan jami’an cibiyar kula da harkokin karatu da hardar kur’ani mai tsarki a yankin Khalil na Palastinu dangane da gasar ku’ani ta Alaqsa da za a gudanar nan gaba a yankin.
Bayanin ya ci gaba da cewa mahalarta zaman sun tattauna hanyoyin da za a inganta wannan gasa da aka saba gudanarwa a tsawon shekaru a cikin dukkanin yankuna na palastinu da ke samun halartar makaranta da kuma mardata da suke karawa da juna, inda akan fitar da matsayi na daya da na biyu da kuma na uku a dukkanin bangarorin gasar tare da bayar da kyuatuka.
Yanzu haka dai an kamala dukkanin shirye-shiryen gasar a cikin yankuna gabar yamma da kogin Jordan da kuma yankin zirin gaza, daga cikin wadanda zsa su halarci gasar har da daliban makarantun kur’ani na yankin, kamar yadda daga bias kuma za a gdanar da wata gasar wadda za ta kebanci jami’an tsaro kawai.
1450088