Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alakhbar Waqi cewa yanzu haka kasashe 20 ne suke halartar wani horo dangane da alkalancin gsar karatun kur’ani mai tsarki kuma ana gudanar da wannan horo ne a kasar saudiyyah kamar yadda aka yi a shekarar da ta gabata.
Bayanin ya ci gaba da cewa ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Saudiyyah ta dauki nauyin wannan horo a reshenta n akula da harkokin kur’ani da kuma shirya gasa, kamar dai yadda babban jami’I a wannan bangare ya sheda, inda ya tabbatar da cewa ya zuwa sun yi nisa wajen aiwatar da shirin, domin kuwa dukkanin wakilan kasashen da suka halarta suna samun horon kamar dai yadda aka sanar da su a cikin horon.
Wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da irin wannan taro na bayar da horo ga alkalan gasar karatun kur’ani da harda ta kasa da kasa, wanda ake gudanarwa akasar Saudiyyah, bayanin y ace dukkanin masu samun horon suna kara fa’idantuwa ne muhimman abubuwa da yakama su sani kuma su kara kiyayewa a yayin alkalancin gasar karatun kur’ani mai tsarki, kasantuwar cewa hakan yana tattare da hadarra masu yawa, da ke bukatar kiyayewa domin yin adalci da kuma yin abin domin Allah.
1451973