Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga bangaren yada labaransa na nahiyar Afirka cewa, karamin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci ta Iran da ke birnin Akra ya fara gudanar da wani shiri na horar maniyyata aikin bana daga kasar Ghana domin sanin hukuncin aikin haji daidai da koyarwar addinin musulunci da kuma koyarwar manzo.
Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da taron tare hadin gwiwa da wasu daga cikin manyan mamalan addinin muslunci na kasar Ghana da suka hada da malam Haj Rashid, wadanda suka bayar da bababr gudunmawa wajen shirya wannan taro wanda karamin ofishin jakadancin na Iran ya dauki nauyinsa baki.
Dukkanin wadanda suka halarci wanann taro na ilmantarwa da fadakarwa kan aikin haji sun nuna gamsuwarsu matuka da irin bayanan da malamai suka yi a wurin, da fatan hakan zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu na haji a wannan shekara.
Tun kafin wannan lokacin dai an samu amincewar mahukuntan kasar Ghana domin gudanar ad duk wasu taruka da za su taimaka wajen wayar wa alhazai kai dangane da aikin haji da kuma yadda ake gudanar das hi.