IQNA

Za A Bude Cibiyoyin Hardar Kur’ani Mai Tsarki 72 A Jamhuriyar Niger

16:34 - September 24, 2014
Lambar Labari: 1453783
Bangaren kasa da kasa, za a bude wasu cibiyoyin kur’ani mai tsarki guda 72 gami da masallatai 230 a fadin jamhuriyar Nijar a wani shiri na karfafawa tare da fadada ayyukan kur’ani mai tsarki a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Al-sharq ta kasar Qatar cewa, ana aikin samar da wasu cibiyoyin kur’ani mai tsarki guda 72 gami da masallatai 230 a fadin jamhuriyar Nijar a cikin wani shiri na karfafawa tare da fadada ayyukan kur’ani mai tsarki a kasar wadda akasarin mazaunanta musulmi ne.
Bayanin ya ci gaba da cewa ya zuwa yanzu an iya gina masallatai 87 gami da cibiyoyin kur’ani mai tsarki guda 41, wadanda dukkaninsu ya zuwa an kamala gina su a sasa daban-daban na kasar domin fara amfani da su nan da yan kwanaki masu zuwa, kuma ana da shirin kamala sauran aikin gina sauran cibiyoyin da makarantun nan da zuwa karshen wannan shekara ta miladiya da muke ciki.
Gwamnatin kasar Qatar ce dai take daukar nauyin gudanar da wannan aiki, kamar dai yadda mahukunta  ajamhuriyar Nijar da kuma ofishin jakadancin Qatar a birnin yamai suka tabbatar da hakan, kamar yadda shi ma babban jami’I mai kula da ayyukan na al’adu a ofishin jakadancin na Qatar a Nijar ya tabbatar, tare da bayyana cewa an riga an ware kudin gudanar da aikin baki daya, kuma da yardarm Allah za a kamala shi kamar dai yadda aka tsara, tare da hadin kai da al’ummar Nijar gami da mahukuntan kasar suke bayarwa.
1452653

Abubuwan Da Ya Shafa: nijar
captcha