IQNA

Ana Kokarin Kare Masallacin Kurduba Daga Fadawa Hannun Majami'a

16:53 - September 27, 2014
Lambar Labari: 1454561
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar kula da harkokin al'adu na addinin muslunci karkashin kungiyar kasashen musulmi na kokarin tattabatar da cewa masallacin Kurduba bai fada hannun majami'a ba.

  Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, wannan kungiyar na kokarin tattabatar da cewa masallacin Kurduba bai fada hannun majami'a ba kamar yadda mahukunta a kasar Spain suke ta kokarin yin hakan. Bayanin ya ci gaba da cewa masallain Kurduba wanda daya ne daga cikin masallatai na tarihi da ake da sua cikin tsoffin daulolin muslunci, a halin yanzu mahukuntan a kasar Spain suna kokarin mika wanann masallaci ga wata babar majami'a a da ke birnin na Kurdata da nufin hade masallacin da wannan majami'a, lamarin day a sanya kungiyoyi a kasashen musulmi mikewa domin tababtar da hakan fat a kasance ba. Tun bayan da muslunci ya isa wasu daga cikin yankunan nahiyar turai, birnin Kurdaba ya zama daya daga cikin biranan turai da ake gudanar da lamurran addini fiye da sauran birane, domin kuwa a samu mutane da suka zama manyan malana addinin muslunci da suka yi rubuce-rubuce a bangarori da dama a cikin wani birni. Kungiyar ISESCO ta sha alwashin dakile wannan shiri na mahukuntan Spain domin kuwa hakan yana matsayin wani babban cin fuska ne ga dukkanin muslumi. 1453778

Abubuwan Da Ya Shafa: Kurduba
captcha