IQNA

Makkah: An Kammala Shirin Haddar Al-Qur'ani Ga Mata A Masallacin Harami

15:22 - July 28, 2025
Lambar Labari: 3493619
IQNA – An kammala karatun haddar kur’ani mai tsarki na mata a masallacin Harami da ke Makkah, inda sama da mahalarta 1,600 suka kammala shirin.

Cibiyar da'arar Al'kur'ani ta mata da ke karkashin babban ofishin kula da harkokin masallatai biyu ne suka shirya wannan shiri. An gudanar da shi a matsayin wani bangare na faffadan ayyukan ilimi da na addini da nufin wadatar da kwarewar mahajjata Umrah.

Kwas din ya yi daidai da tsarin gudanar da aikin Hajjin bana na lokacin Umrah, tare da mai da hankali kan taimaka wa maziyarta su shagaltu da karatun kur'ani a cikin ruhi.

An fara gudanar da shirin ne a ranar 25 ga watan Zul-Hijja, shekara ta 1446 bayan hijira, inda aka tara mahalarta mata 1,602 daga da'irar karatun kur'ani mai tsarki guda 62, wanda aka kasu kashi uku na koyarwa.

An kammala kwas din tare da dalibai 55 da suka kammala karatun kur’ani mai tsarki ta hanyar amfani da karatuttuka daban-daban (qira’at). Wani bangare na kwas din ya mayar da hankali kan karfafa haddar, tare da mahalarta mata 140 sun kammala karatun cikakken karatu biyu.

Kwararrun malamai mata da kwararrun karatun kur’ani ne suka jagoranci zaman, inda suka ba da umarni da aka tsara a duk tsawon shirin.

Wannan shiri dai wani bangare ne na kamfen da mahukuntan Masallacin Harami da na Masjidul Nabawi ke ci gaba da yi na inganta cudanya da kur’ani, da fadada hanyoyin samun ilimin addini da kuma tallafa wa harkokin karatun kur’ani a cikin masallatai biyu masu alfarma.

 

4296748

 

 

captcha