Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-badil cewa, a cikin wannan mako an samu kwafin wani tsohon kur'ani mai tsarki a hannun wani daya daga cikin malaman marakantar sakandare ta kur'ani a garin tanta na kasar ta Masar mai suna Usama Muhammad Muhyiddin Alhussaini.
Malamin ya ce ya samu wannan kur'ani ne daga hannun mahaifinsa wanda ya rasu a cikin shekara ta 1970, wanda kuma shi ma ya same shi ne daga mahaifinsa wanda ya rasu tun a cikin shekara ta 1990, kuma ya samu wannan kwafin kur'ani ne a lokacin da yaje aikin waccan shekara, inda har yanzu yaya da jikoki suke ci gaba da ajiye wannan kur'ani mai tsarki.
Ya ci gaba da cewa an rubuta wannan kur'ani ne da hannu, kuma an rarraba shi zuwa izihi da kuma juzu'I, wanda hakan zai bai wa mai karatu damar samun sauki wajen karatunsa, kamar yadda aka yi amfani da abubuwan rubutu masu kyaun gaske da suka tawada mai kaloli wajen wasali da wakafi da sauran lamomi na kur'ani da ke taimaka mai karatu.
Usama Muhammad Muhyiddin Alhussaini ya kara da cewa zai ci gaba da ajiye wannan kwafin kur'ani, duk kuwa da cewa ajiye abubuwan tarihi irin wadannan masu kima na bukatar masani da gogewa a kan hakan.