Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shi da Muhammad Anas Alarabi Al-qabbani daya daga cikin alkalan gasar kasaru da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa ya bukaci da fitar da wasu daga cikin irin ayyukan jamhuriyar muslunci a bangarori na tattalin arzki da zamantakewa da ci gaban ilimi a lokacin gudanar da gasar kur’ani ta daliban jami’a.
Alkalin ya ci gaba da cewa jamhuriyar muslunci ta Iran tana taka gagarumar rawa abangarori da dama da ya kamata a ce musulmi da kuma dalbai na makarantun kur’ani ko kuma masu gudanar da harkokinsu a wannan bangaren da suke shiga gasa ta kasa da kasa suna da masaniya, domin sanin hanyoyin da su ma za su afana da hakan, musamman ma dai gasar da ake gudanarwa a cikin jamhiriyar muslunci ta Iran ta kasa da kasa.
Ya ci gaba da cewa akwai makaranta da mahardta da suka halarci gasar kur’ani da ake gudanarwa a kasar Iran daga kasashen duniya, wadanda suka nuna matukar bukatar hakan, domin kuwa ko babu komai yana nasa babban tasirin domin sanin irin ci gaban da kasar da take bin irin wannan tsari take da shi, domin tabbatar wa duniya cewa za a iya samun ci gaba a dukkanin bangarori na ilimi na zamani da kuma na addini.